Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 9:7-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Dawuda ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama zan yi maka alheri ne saboda mahaifinka, Jonatan. Zan mayar maka da dukan gonakin kakanka, Saul. Kullum kuma za ka riƙa cin abinci a teburina.”

8. Mefiboshet kuwa ya rusuna, ya ce, “Ni wane ne har da za ka kula da ni, ni da ban fi mataccen kare daraja ba?”

9. Sa'an nan sarki ya kira Ziba, baran Saul, ya ce masa, “Dukan abin da yake na Saul, da dukan abin da yake na iyalinsa, na ba ɗan maigidanka.

10. Kai, da 'ya'yanka maza, da barorinka za ku riƙa yi wa iyalin Saul noma, ku kawo musu amfanin domin su sami abinci, amma Mefiboshet kansa, zai riƙa cin abinci a teburina kullum.” (Ziba kuwa yana da 'ya'ya maza goma sha biyar, da barori ashirin.)

11. Ziba ya amsa wa sarki, ya ce, “Baranka zai yi dukan abin da sarki ya umarta.”Mefiboshet kuwa ya riƙa cin abinci a teburin sarki kamar ɗaya daga cikin 'ya'yan sarkin.

12. Mefiboshet yana da ɗa sunansa Mika. Dukan waɗanda suke zaune a gidan Ziba kuma suka zama barorin Mefiboshet.

Karanta cikakken babi 2 Sam 9