Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 9:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sa'an nan sarki ya tambaye shi ko akwai wani wanda ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna masa alherin Allah.Ziba ya ce wa sarki, “Akwai ɗan Jonatan, gurgu ne kuwa.”

4. Sai sarki ya tambaye shi, “Ina yake?”Ziba ya ce, “Yana gidan Makir, ɗan Ammiyel a Lodebar.”

5. Sarki kuwa ya aika aka zo da shi daga gidan Makir, ɗan Ammiyel, daga Lodebar.

6. Da aka zo da Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, sai ya rusuna har ƙasa, ya yi gaisuwa. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!”Ya amsa, “Ranka ya daɗe, ga baranka.”

7. Dawuda ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama zan yi maka alheri ne saboda mahaifinka, Jonatan. Zan mayar maka da dukan gonakin kakanka, Saul. Kullum kuma za ka riƙa cin abinci a teburina.”

8. Mefiboshet kuwa ya rusuna, ya ce, “Ni wane ne har da za ka kula da ni, ni da ban fi mataccen kare daraja ba?”

9. Sa'an nan sarki ya kira Ziba, baran Saul, ya ce masa, “Dukan abin da yake na Saul, da dukan abin da yake na iyalinsa, na ba ɗan maigidanka.

Karanta cikakken babi 2 Sam 9