Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 6:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dawuda kuma ya tattara zaɓaɓɓun mutane dubu talatin (30,000) na Isra'ila.

2. Sai ya tafi tare da su duka zuwa Kiriyat-yeyarim domin ya kawo akwatin Alkawarin Allah, wanda ake kira da sunan Ubangiji Mai Runduna wanda yake zaune a tsakanin kerubobin.

3-4. Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Suka sa akwatin alkawari a sabuwar karusa. Uzza da Ahiyo, 'ya'yan Abinadeb, maza, suka bi da karusar da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo ne yake tafiya a gaban akwatin alkawarin.

5. Sai Dawuda da Isra'ilawa duka suka yi rawa sosai don farin ciki a gaban Ubangiji. Aka yi ta raira waƙoƙi, ana kaɗa molaye, da garayu, da goge, da kacakaura, da kuge.

6. Da suka zo masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa ya riƙa akwatin alkawarin Allah, gama takarkaran sun yi kwarangyasa.

7. Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take kusa da akwatin alkawarin Allah, saboda ya taɓa akwatin alkawari.

8. Sai Dawuda ya ji haushi domin Ubangiji ya fashe haushinsa a kan Uzza. Aka sa wa wurin suna Feresauzza har wa yau.

9. Dawuda kuwa ya ji tsoron Ubangiji a ran nan, ya ce, “Ƙaƙa zan ajiye akwatin alkawarin Ubangiji a wurina?”

10. Domin haka Dawuda bai yarda ya kai akwatin alkawarin Ubangiji cikin Birnin Dawuda ba, sai ya kai shi gidan Obed-edom Bagitte.

11. Akwatin alkawarin Ubangiji yana a gidan Obed-edom Bagitte har wata uku. Ubangiji kuwa ya sa wa Obed-edom da dukan iyalinsa albarka.

12. Aka faɗa wa Dawuda sarki, cewa, Ubangiji ya sa wa gidan Obed-edom albarka, da dukan abin da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Sai Dawuda ya tafi da murna ya kawo akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-edom zuwa Birnin Dawuda.

Karanta cikakken babi 2 Sam 6