Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 5:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Hiram Sarkin Taya ya aiki jakadu zuwa wurin Dawuda. Ya kuma aika masa da katakan itacen al'ul, da kafintoci, da masu yin gini da duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda gida.

12. Dawuda kuwa ya gane lalle Ubangiji ya tabbatar da shi sarki bisa jama'ar Isra'ila, ya kuma ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa, Isra'ila.

13. Bayan zuwan Dawuda Urushalima daga Hebron, sai ya ɗauki waɗansu ƙwaraƙwarai, ya kuma auri waɗansu mata. Aka kuma haifa masa waɗansu 'ya'ya mata da maza.

14. Sunayen 'ya'yan da aka haifa masa a Urushalima ke nan, Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu,

15. da Ibhar, da Elishuwa, da Nefeg, da Yafiya,

16. da Elishama, da Eliyada, da Elifelet.

17. Sa'ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila, sai dukansu suka haura zuwa neman ran Dawuda. Da Dawuda ya ji Filistiyawa suna nemansa, sai ya gangara zuwa kagara.

18. Filistiyawa kuwa suka zo suka bazu a kwarin Refayawa.

19. Dawuda kuwa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?”Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka haura, gama hakika, zan ba da Filistiyawa a hannunka.”

Karanta cikakken babi 2 Sam 5