Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 4:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Ish-boshet, ɗan Saul, ya ji labari Abner ya mutu a Hebron, sai gabansa ya faɗi. Dukan mutanen Isra'ila kuma suka tsorata.

2. Shi ɗan nan na Saul yana da shugabanni biyu na 'yan hari, su ne Ba'ana da Rekab, 'ya'yan Rimmon na ƙasar Biliyaminu daga Biyerot, (gama an lasafta Biyerot cikin yankin ƙasar Biliyaminu.

3. Mutanen Biyerot sun gudu zuwa Gittayim inda suke zaman baƙunci har wa yau.)

4. Jonatan, ɗan Saul kuwa, yana da ɗa, sunansa Mefiboshet, amma gurgu ne. Yana da shekara biyar sa'ad da aka kawo labarin mutuwar Saul da Jonatan daga Yezreyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi, ta sheƙa a guje. A sa'ad da take gudu sai ya faɗo, sanadin gurguntakar ke nan.

5. Rekab da Ba'ana 'ya'yan Rimmon suka tafi gidan Ish-boshet da tsakar rana, a lokacin da yake shaƙatawa.

Karanta cikakken babi 2 Sam 4