Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 3:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Gidan Saul da gidan Dawuda suka daɗe suna yaƙi da juna. Ƙarfin gidan Dawuda ya yi ta ƙaruwa, amma na gidan Saul ya yi ta raguwa.

2. 'Ya'ya maza da aka haifa wa Dawuda a Hebron ke nan, Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa ɗan farinsa, Amnon.

3. Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom.

4. Haggit ta haifa masa ɗansa na huɗu, Adonaija. Abital ta haifa masa ɗansa na biyar, Shefatiya.

5. Matarsa Egla ta haifa masa ɗansa na shida, Itireyam. Dukan waɗannan a Hebron ne aka haife su.

6. Abner ya ƙasaita sosai a gidan Saul a lokacin da ake yaƙi tsakanin jarumawan Saul da na Dawuda.

7. Saul yana da ƙwarƙwara mai suna Rizfa, 'yar Aiya. Sai Ish-boshet ya ce wa Abner, “Me ya sa ka kwana da ƙwarƙwarar tsohona?”

Karanta cikakken babi 2 Sam 3