Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 23:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. shi kuwa ya tsaya, ya yi ta yaƙi da Filistiyawa, har hannunsa ya ƙage, har bai iya ɓanɓaruwa daga takobinsa ba. Ubangiji ya ba da babbar nasara a wannan rana. Bayan an gama sai Isra'ilawa suka koma wurin Ele'azara don su kwashi ganima kawai.

11. Biye da Ele'azara kuma, sai Shamma, ɗan Agi, daga Harod. Filistiyawa suka taru a Lihai, inda akwai wata gonar wake. Isra'ilawa kuwa suka guji wa Filistiyawa.

12. Amma Shamma ya tsaya a tsakiyar gonar, ya kāre ta. Ya kuma kashe Filistiyawa. Ubangiji ya ba da babbar nasara.

13. Sai jarumawa uku daga cikin jarumawa talatin, suka tafi wurin Dawuda a kogon Adullam, gab da lokacin girbi. A lokacin kuwa Filistiyawa sun kafa sansani a kwarin Refayawa.

14. Dawuda yana cikin kagara, ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuwa tana a Baitalami.

15. Dawuda ya ji marmari, ya ce, “Kai, da ma wani zai ba ni ruwan rijiyar ƙofar garin Baitalami in sha!”

16. Shahararrun jarumawan nan uku kuwa suka sheƙa a guje, suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka tafi, suka ɗebo ruwa daga rijiyar ƙofar garin Baitalami, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda bai sha ba, ya zuba shi hadaya a gaban Ubangiji.

17. Sa'an nan ya ce, “Ya Ubangiji, ka tsare ni daga shan jinin mutanen da suka sadaukar da ransu.” Saboda haka bai sha ruwan ba.Abubuwan da jarumawan nan uku suka yi ke nan.

18. Abishai, ɗan'uwan Yowab ɗan Zeruya, shi ne shugaban jarumawan nan talatin. Sa'ad da ya girgiza mashinsa, sai da ya kashe mutum ɗari uku. Da haka ya samar wa kansa sūna tare da mutanen nan uku.

Karanta cikakken babi 2 Sam 23