Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 23:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan ita ce maganar Dawuda ta ƙarshe. Dawuda ɗan Yesse, shi ne mutumin da Allah ya ɗaukaka, wanda Allah na Yakubu ya zaɓa ya zama sarki, wanda kuma ya shirya waƙoƙin Isra'ila. Dawuda ya ce,

2. “Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina,Saƙonsa yana kan leɓunana.

3. Allah na Isra'ila ya yi magana,Matsaron Isra'ila ya ce mini,‘Sarkin da yake mulkin mutane da adalci,Wanda yake mulki da tsoron Allah,

4. Yana kama da hasken rana a kan girgijen alfijir,Rana da take sa ciyawa ta yi ƙyalƙyali bayan an gama ruwan sama.’

5. “Haka Allah zai sa wa zuriyata albarka,Gama ya yi mini madawwamin alkawari,Duka kuwa a shirye yake, zai kuwa kiyaye.Abin da nake bukata ke nan,Wannan ne nasarata,Na tabbata kuwa Allah zai kammala shi.

6. Amma marasa Allah suna kama da ƙayayuwan da aka zubar,

7. Amma wanda zai taɓa su, sai da wani ƙarfe ko da māshi,Za a ƙone su ƙurmus.”

8. Ga sunayen jarumawan Dawuda, Yosheb-basshebet, daga Takemon, shi ne ɗaya daga cikin shugabanni uku. Ya girgiza māshinsa, ya kashe mutum ɗari takwas baki ɗaya.

9. Wanda yake biye da shi a cikin su uku ɗin shi ne Ele'azara, ɗan Dodo, ɗan Ahowa. Yana tare da Dawuda sa'ad da suka raina Filistiyawan da suka taru don yaƙi. Mutanen Isra'ila kuwa suka jā baya,

10. shi kuwa ya tsaya, ya yi ta yaƙi da Filistiyawa, har hannunsa ya ƙage, har bai iya ɓanɓaruwa daga takobinsa ba. Ubangiji ya ba da babbar nasara a wannan rana. Bayan an gama sai Isra'ilawa suka koma wurin Ele'azara don su kwashi ganima kawai.

11. Biye da Ele'azara kuma, sai Shamma, ɗan Agi, daga Harod. Filistiyawa suka taru a Lihai, inda akwai wata gonar wake. Isra'ilawa kuwa suka guji wa Filistiyawa.

Karanta cikakken babi 2 Sam 23