Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 19:4-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sarki ya rufe fuskarsa, ya yi kuka da ƙarfi, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ya Absalom, ɗana, ɗana!”

5. Yowab kuwa ya tafi wurin sarki a gidansa ya ce, “Yau ka kunyatar da mutanenka duka waɗanda suka ceci ranka, da rayukan 'ya'yanka mata da maza, da rayukan matanka, da rayukan ƙwaraƙwaranka.

6. Gama kana ƙaunar maƙiyanka, amma kana ƙin waɗanda suke ƙaunarka. Gama yau ka bayyana a fili, shugabannin sojojinka da fādawanka ba a bakin kome suke a gare ka ba. Gama yau na gane da a ce Absalom yana da rai, mu kuwa muka mutu duka, da daɗi za ka ji.

7. Don haka sai ka tashi yanzu, ka fita ka yi wa mutanenka magana mai daɗi. Gama na rantse da Ubangiji idan ba ka fita ba, ba wanda zai zauna tare da kai da daren nan. Wannan kuwa zai fi muni fiye da kowane irin mugun abin da ya taɓa samunka tun daga ƙuruciyarka har zuwa yanzu.”

8. Sa'an nan sarki ya tashi, ya zauna a dandalin ƙofar garu. Aka faɗa wa mutanensa duka, cewa, ga sarki yana zaune a dandalin ƙofar garu. Mutanensa duka kuwa suka zo suka kewaya sarki.Bayan wannan sai dukan Isra'ilawa suka gudu, kowa ya tafi gidansa.

9. Dukan mutanen ƙasar Isra'ila suna ta jayayya, suna cewa, “Sarki Dawuda ne ya cece mu daga hannun abokan gabanmu, ya cece mu daga hannun Filistiyawa, to, ga shi, ya gudu daga ƙasar don ya tsere wa Absalom.

10. Ga shi kuma, Absalom ɗin da muka naɗa ya zama sarkinmu, an kashe shi a yaƙi. Yanzu fa, me ya sa muka yi shiru ba mu komo da sarki ba?”

11. Da labarin abin da Isra'ilawa suke cewa, ya zo gun sarki Dawuda, sai ya aika zuwa wurin firistoci, wato Zadok da Abiyata, a faɗa musu su tambayi dattawan Yahuza abin da ya sa suka zama na ƙarshe a kan komar da sarki a gidansa.

12. Ya ce, “Ai, ku 'yan'uwana ne, da ƙasusuwana, da namana. To, me ya sa za ku zama na ƙarshe a kan komar da sarki?

13. Ku ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba ƙashina da namana ba ne? Allah ya hukunta ni idan ba kai ne shugaban rundunar sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”

14. Da haka Dawuda ya rinjayi zukatan mutanen Yahuza, suka zama ɗaya, kamar mutum guda. Sai suka aika wurin sarki, cewa, ya komo tare da dukan fādawansa.

15. Sa'ad da sarki ya iso Urdun. Mutanen Yahuza suka tafi Gilgal suka taryi sarki, domin su hawo da shi Urdun.

16. Shimai ɗan Gera kuma, mutumin Biliyaminu daga Bahurim, ya gaggauta, ya gangara tare da mutanen Yahuza don ya taryi sarki Dawuda.

Karanta cikakken babi 2 Sam 19