Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 15:11-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Mutum metan waɗanda ya gayyata daga Urushalima suka tafi tare da shi da zuciya ɗaya ba tare da sanin kome ba.

12. Lokacin da Absalom yake miƙa hadaya, sai ya aika zuwa Gilo a kira masa Ahitofel Bagilone mai ba Dawuda shawara. Maƙarƙashiyar kuwa ta yi ƙarfi. Mutane masu haɗa kai da Absalom suka riƙa ƙaruwa kullum.

13. Ana nan sai wani manzo ya zo wurin Dawuda, ya ce masa, “Zukatan mutanen Isra'ila suna wajen Absalom.”

14. Sa'an nan Dawuda ya ce wa fādawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Mu tashi mu gudu, in ba haka ba ko ɗayanmu ba zai tsere daga hannun Absalom ba. Sai mu hanzarta mu gudu don kada ya tarar da mu, ya yi mana ɓarna, ya kuma kashe kowa da kowa a birnin.”

15. Fādawan suka ce, “Mu a shirye muke mu yi dukan abin da ubangijinmu sarki ya faɗa.”

16. Sarki ya fita, iyalinsa suka bi shi, amma ya bar ƙwaraƙwarai goma su lura da gidan.

17. Sarki ya fita yana tafiya da ƙafa, dukan mutane kuwa suna biye da shi. Da suka zo Bet-Merhak, wato gida na ƙarshe sai suka tsaya.

18. Dukan fādawansa, da matsaransa, wato dukan Keretiyawa, da dukan Feletiyawa, da dukan Gittiyawa, sojoji ɗari shida waɗanda suka bi Dawuda tun daga Gat suka wuce a gabansa.

19. Sarki kuwa ya ce wa Ittayi, shugabansu, “Don me kai kuma za ka tafi tare da mu? Koma ka zauna wurin sabon sarki, gama kai baƙo ne, ɗan gudun hijira kuma daga ƙasarku.

20. Jiya jiya ka zo, ba daidai ba ne in sa ka ka yi ta ragaita tare da mu, ga shi, ban san inda zan tafi ba. Koma tare da 'yan'uwanka. Ubangiji ya nuna maka alherinsa, da amincinsa.”

Karanta cikakken babi 2 Sam 15