Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 10:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Sarkin Ammonawa, wato Nahash, ya rasu, sai Hanun ɗansa ya gāje shi.

2. Dawuda ya ce, “Zan yi wa Hanun alheri kamar yadda tsohonsa ya yi mini.” Dawuda kuwa ya aiki manzanni su yi masa ta'aziyya.Amma da suka isa can,

3. sai hakiman Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama tsohonka ne, da ya aiko manzanninsa su yi maka ta'aziyya? Ai, manzannin nan da ya aiko 'yan leƙen asirin ƙasa ne. Sun zo ne su bincika don su san yadda za a ci birnin.”

4. Sai Hanun ya sa aka aske wa manzannin nan na Dawuda rabin gyammansu suka kuma yanyanke rigunansu daidai ɗuwawu, sa'an nan suka sallame su.

5. Da aka faɗa wa Dawuda sai ya aika a tarye su, gama mutanen sun sha kunya ƙwarai. Sarki Dawuda ya ce musu su zauna a Yariko har gyammansu su toho, sa'an nan su komo.

6. Da Ammonawa suka ga sun sa Dawuda ya yi gāba da su, suka yi sufurin Suriyawan Bet-rehob da na Zoba, mutum dubu ashirin (20,000), suka kuma yi sufurin Sarkin Ma'aka da mutanensa dubu ɗaya, da mutanen Ish-tobi dubu goma sha biyu (12,000).

7. Da Dawuda ya ji labari, sai ya aiki Yowab da dukan rundunar jarumawan.

Karanta cikakken babi 2 Sam 10