Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 1:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan rasuwar Saul, sa'ad da Dawuda ya komo daga karkashe Amalekawa, ya yi kwana biyu a Ziklag.

2. Kashegari sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Saul, da tufafinsa a yayyage, da ƙura kuma a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi ƙasa, ya yi gaisuwa.

3. Sai Dawuda ya tambaye shi, ya ce, “Daga ina ka zo?”Ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra'ilawa.”

4. Dawuda ya ce masa, “Faɗa mini abin da ya faru.”Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga bakin dāga, an kuma kashe galibin mutanenmu. Saul da ɗansa Jonatan kuma sun mutu.”

5. Dawuda ya ce wa mutumin, “Ta yaya ka sani Saul da ɗansa, Jonatan, sun mutu?”

6. Mutumin kuwa ya amsa ya ce, “Ya zama fa ina kan dutsen Gilbowa, sai ga Saul ya jingina a māshinsa. Karusai da mahayan dawakan abokan gāba sun rutsa shi.

7. Da ya waiga, ya gan ni, sai ya kira ni, ni kuwa na amsa, na ce, ‘Ga ni.’

8. Ya ce mini, ‘Wane ne kai?’ Na ce masa, ‘Ni Ba'amaleke ne.’

9. Sai ya ce mini, ‘Zo ka kashe ni gama ina cikin azaba, amma raina bai fita ba.’

10. Sai na tafi na kashe shi domin na tabbata ba zai yi rai ba bayan ya fāɗi. Na kuma cire kambin da yake kansa da ƙarau da yake a dantsensa. Ga su, na kawo wa ubangijina.”

11. Sai Dawuda ya yayyage tufafinsa. Dukan mutanen da suke tare da shi kuma suka yayyage nasu.

12. Suka yi makoki, da kuka, da azumi har maraice saboda Saul, da Jonatan ɗansa, da mutanen Ubangiji, da gidan Isra'ila domin an Karkashe su a yaƙi.

13. Dawuda ya ce wa mutumin nan da ya kawo labarin, “Daga ina ka zo?”Sai ya ce masa, “Ai, ni ɗan wani baƙo ne, Ba'amaleke.”

14. Dawuda ya ce, “Me ya sa ba ka ji tsoro ka miƙa hannunka, ka hallaka wanda Ubangiji ya keɓe ba?”

Karanta cikakken babi 2 Sam 1