Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 7:24-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. 'Yarsa kuma ita ce Sheyera, wadda ta gina garin Bet-horon na kwari da na tudu, ta kuma gina Uzzen-sheyera.

25. Waɗansu zuriyarsa bi da bi, su ne Refa, da Reshe, da Tela, da Tahan,

26. da Ladan, da Ammihud, da Elishama,

27. da Nun, da Joshuwa.

28. Mallakarsu da wuraren zamansu, su ne Betel duk da garuruwanta, da Nayaran wajen gabas, da Gezer wajen yamma duk da garuruwanta, da Shekem duk da garuruwanta, har zuwa Ayya duk da garuruwanta.

29. Zuriyar Manassa sun mallaki Bet-sheyan, da Ta'anak, da Magiddo, da Dor duk da garuruwan da suke kewaye da su. A nan ne zuriyar Yusufu, ɗan Isra'ila, suka zauna.

30. 'Ya'yan Ashiru, maza, su ne Yimna, da Yishuwa, da Yishwi, da Beriya, da 'yar'uwarsu Sera.

31. 'Ya'yan Beriya, maza, su ne Eber, da Malkiyel wanda ya kafa garin Birzayit.

32. Eber shi ne mahaifin Yaflet, da Shemer, da Helem, da 'yar'uwarsu Shuwa.

33. 'Ya'yan Yaflet, maza, su ne Fasak, da Bimhal, da Ashewat.

34. 'Ya'yan Shemer maza, su ne Ahi, da Roga, da Yehubba, da Aram.

35. 'Ya'ya maza na ɗan'uwansa Helem, su ne Zofa, da Imna, da Sheles da Amal.

36. 'Ya'yan Zofa, su ne Suwa, da Harnefer, da Shuwal, da Beri, da Imra,

37. da Bezer, da Hod, da Shamma, da Shilsha, da Yeter, da Biyera.

38. 'Ya'yan Yeter, su ne Yefunne, da Fisfa, da Ara.

39. 'Ya'yan Ulla, maza, su ne Ara, da Haniyel, da Riziya.

40. Waɗannan duka su ne zuriyar Ashiru, su ne kuma shugabannin gidajen kakanninsu. Zaɓaɓɓun jarumawa ne su, manyan sarakuni. Yawansu da aka lasafta bisa ga asalinsu don yaƙi su dubu ashirin da dubu shida ne (26,000).

Karanta cikakken babi 1 Tar 7