Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 7:1-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. 'Ya'yan Issaka, maza, su huɗu ne, wato Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron.

2. 'Ya'yan Tola, maza, su ne Uzzi, da Refaya, da Yeriyel, da Yamai, da Ibsam, da Sama'ila, su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Tola kuwa manyan mayaƙa ne a zamaninsu. Yawansu a zamanin Dawuda, su dubu ashirin da biyu ne da ɗari shida (22,600).

3. Ɗan Uzzi, shi ne Izrahiya. 'Ya'yan Izrahiya, maza, su ne Maikel, da Obadiya, da Yowel, da Isshiya. Su biyar duka manyan mutane ne.

4. A zamaninsu, bisa ga gidajen kakanninsu suna da sojoji dubu talatin da dubu shida (36,000) gama suna da mata da yara da yawa.

5. Mayaƙan da aka lasafta bisa ga asalinsu na dukan iyalan Issaka, su dubu tamanin da dubu bakwai ne (87,000), jarumawa ne sosai.

6. 'Ya'yan Biliyaminu su uku ne, wato Bela, da Beker, da Yediyayel.

7. 'Ya'yan Bela, maza, su biyar ne, wato Ezbon, da Uzzi, da Uzziyel, da Yerimot, da Iri. Su ne shugabannin gidajen kakanninsu, jarumawa ne su. An lasafta su bisa ga asalinsu, su dubu ashirin da biyu ne da talatin da huɗu (22,034).

8. 'Ya'yan Beker, maza, su ne Zemira, da Yowash, da Eliyezer, da Eliyehoyenai, da Omri, da Yerimot, da Abaija da Anatot, da Alamet. Waɗannan duka 'ya'yan Beker ne, maza.

9. An lasafta su bisa ga asalinsu a zamaninsu, su dubu ashirin ne da ɗari biyu (20,200), jarumawa ne su sosai. Su ne kuma shugabannin gidajen kakanninsu.

10. Ɗan Yediyayel shi ne Bilhan. 'Ya'yan Bilhan, maza, su ne Yewush, da Biliyaminu, da Ehud, da Kena'ana, da Zetan, da Tarshish, da Ahishahar.

11. Duk waɗannan 'ya'yan Yediyayel, maza ne, bisa ga shugabannin gidajen kakanninsu. Su dubu goma sha bakwai ne da ɗari biyu (17,200), jarumawa ne sosai, shiryayyu don yaƙi.

12. Shuffim da Huffim su ne 'ya'yan Iri, maza.Hushim shi ne ɗan Ahiram.

13. Naftali yana da 'ya'ya huɗu, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum. Su ne zuriya daga Bilha.

14. 'Ya'yan Manassa, maza, su ne Asriyel, wanda ƙwarƙwararsa Ba'aramiya ta haifa masa. Ta kuma haifi Makir mahaifin Gileyad.

15. Makir ya auro wa Huffim da Shuffim mata. Sunan 'yar'uwarsa Ma'aka, sunan ɗan'uwansa kuwa Zelofehad, Zelofehad yana da 'ya'ya mata kaɗai.

16. Sai Ma'aka matar Makir ta haifi ɗa, ta sa masa suna Feres, sunan ɗan'uwansa kuwa Sheres. 'Ya'yan Feres maza, su ne Ulam da Rakem.

17. Ɗan Ulam shi ne Bedan. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Gileyad ɗan Makir, jīkan Manassa.

18. 'Yar'uwarsa, Hammoleket ta haifi Ishodi, da Abiyezer, da Mala.

Karanta cikakken babi 1 Tar 7