Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 6:57-71 Littafi Mai Tsarki (HAU)

57. Suka ba 'ya'yan Haruna, maza, biranen mafaka, wato Hebron, da Libna tare da makiyayarta, da Yattir, da Eshtemowa tare da makiyayarta,

58. da Holon tare da makiyayarta, da Debir tare da makiyayarta,

59. da Ayin tare da makiyayarta, da Bet-shemesh tare da makiyayarta.

60. Daga kabilar Biliyaminu aka ba su Geba tare da makiyayarta, da Allemet tare da makiyayarta, da Anatot tare da makiyayarta. Dukan biranen iyalansu guda goma sha uku ne.

61. Aka ba sauran 'ya'yan Kohat, maza, garuruwa goma daga na rabin kabilar Manassa, ta hanyar kuri'a.

62. Aka kuma ba Gershonawa bisa ga iyalansu, birane goma sha uku daga na kabilar Issaka, da na kabilar Ashiru, da na kabilar Naftali, da na kabilar Manassa da take nan a Bashan.

63. Haka kuma aka ba 'ya'yan Merari, maza, bisa ga iyalansu, garuruwa goma sha biyu daga na kabilar Ra'ubainu, da na kabilar Gad, da na kabilar Zabaluna.

64. Haka fa, jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa garuruwa duk da makiyayansu.

65. Daga na kabilar Yahuza, da na kabilar Saminu, da na kabilar Biliyaminu kuma aka ba da waɗannan garuruwan da aka ambaci sunayensu ta hanyar kuri'a.

66. Waɗansu daga cikin iyalan 'ya'yan Kohat, maza, sun sami garuruwa na yankinsu daga cikin kabilar Ifraimu.

67. Sai suka ba su waɗannan biranen mafaka, wato Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu duk da makiyayarta, da Gezer tare da makiyayarta,

68. da Yokmeyam duk da makiyayarta, da Bet-horon duk da makiyayarta,

69. da Ayalon duk da makiyayarta, da Gatrimmon duk da makiyayarta.

70. Daga cikin rabin kabilar Manassa kuma an ba su Ta'anak duk da makiyayarta, da Bileyam duk da makiyayarta. An ba da waɗannan ga sauran iyalai na 'ya'yan Kohat, maza.

71. Daga na rabin kabilar Manassa na gabas, an ba 'ya'yan Gershon, maza, Golan ta Bashan tare da makiyayarta, da Ashtarot duk da makiyayarta.

Karanta cikakken babi 1 Tar 6