Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 6:54-63 Littafi Mai Tsarki (HAU)

54. Ga wuraren da aka ba zuriyar Haruna, na iyalin Kohat. Sun karɓi rabo na farko a ƙasar.

55. Rabonsu ya haɗu da Hebron ta yankin ƙasar Yahuza, da makiyayar da suke kewaye da ita.

56. Amma an ba Kalibu ɗan Yefunne saurukan birnin, tare da ƙauyukansa.

57. Suka ba 'ya'yan Haruna, maza, biranen mafaka, wato Hebron, da Libna tare da makiyayarta, da Yattir, da Eshtemowa tare da makiyayarta,

58. da Holon tare da makiyayarta, da Debir tare da makiyayarta,

59. da Ayin tare da makiyayarta, da Bet-shemesh tare da makiyayarta.

60. Daga kabilar Biliyaminu aka ba su Geba tare da makiyayarta, da Allemet tare da makiyayarta, da Anatot tare da makiyayarta. Dukan biranen iyalansu guda goma sha uku ne.

61. Aka ba sauran 'ya'yan Kohat, maza, garuruwa goma daga na rabin kabilar Manassa, ta hanyar kuri'a.

62. Aka kuma ba Gershonawa bisa ga iyalansu, birane goma sha uku daga na kabilar Issaka, da na kabilar Ashiru, da na kabilar Naftali, da na kabilar Manassa da take nan a Bashan.

63. Haka kuma aka ba 'ya'yan Merari, maza, bisa ga iyalansu, garuruwa goma sha biyu daga na kabilar Ra'ubainu, da na kabilar Gad, da na kabilar Zabaluna.

Karanta cikakken babi 1 Tar 6