Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 5:6-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. da Biyera wanda Tiglat-filesar Sarkin Assuriya ya kai bauta. Shi ne shugaban Ra'ubainawa.

7. Danginsa bisa ga iyalansu da asalinsu a zamaninsu, su ne sarki Yehiyel, da Zakariya,

8. da Bela ɗan Azaz, wato jīkan Shema, ɗan Yowel, wanda ya zauna a Arower har zuwa Nebo da Ba'al-meyon.

9. Ya kuma zauna wajen gabas, har zuwa goshin jejin da yake wajen Kogin Yufiretis, saboda shanunsu sun ƙaru a ƙasar Gileyad.

10. Zuriyar Ra'ubainu suka yi yaƙi da Hagarawa a kwanakin Saul. Suka ci Hagarawa, saboda haka suka zauna a ƙasar da take gabashin Gileyad.

11. 'Ya'yan Gad, maza, suka zauna a ƙasar Bashan, daura da Ra'ubainawa har zuwa Salka.

12. Yowel ne sarki, Shafam kuwa shi ne na biyun, da Yanai, da Shafat, su ne tushen Bashan.

13. Danginsu bisa ga gidajen kakanninsu, su ne Maikel, da Meshullam, da Sheba, da Yorai, da Jakan, da Ziya, da Eber, su bakwai ke nan.

14. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Abihail ɗan Huri. Ga yadda kakanninsu suke, wato Abihail, ɗan Huri ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Maikel, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.

15. Ahi ɗan Abdiyel, wato jīkan Guni, shi ne shugaban gidan kakanninsu.

16. Suka zauna a Gileyad, da Bashan, da garuruwanta, da dukan iyakar makiyayar Sharon.

17. (An rubuta waɗannan duka bisa ga asalinsu a zamanin Yotam, Sarkin Yahuza, da Yerobowam Sarkin Isra'ila.)

18. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa suna da jarumawa masu riƙon garkuwa da takobi, masu harbi kuma da baka. Gwanayen yaƙi ne, su dubu arba'in da huɗu, da ɗari bakwai da sittin ne (44,760).

19. Suka yi yaƙi da Hagarawa, da Yetur, da Nafish, da Nodab.

Karanta cikakken babi 1 Tar 5