Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 5:12-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Yowel ne sarki, Shafam kuwa shi ne na biyun, da Yanai, da Shafat, su ne tushen Bashan.

13. Danginsu bisa ga gidajen kakanninsu, su ne Maikel, da Meshullam, da Sheba, da Yorai, da Jakan, da Ziya, da Eber, su bakwai ke nan.

14. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Abihail ɗan Huri. Ga yadda kakanninsu suke, wato Abihail, ɗan Huri ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Maikel, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.

15. Ahi ɗan Abdiyel, wato jīkan Guni, shi ne shugaban gidan kakanninsu.

16. Suka zauna a Gileyad, da Bashan, da garuruwanta, da dukan iyakar makiyayar Sharon.

17. (An rubuta waɗannan duka bisa ga asalinsu a zamanin Yotam, Sarkin Yahuza, da Yerobowam Sarkin Isra'ila.)

18. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa suna da jarumawa masu riƙon garkuwa da takobi, masu harbi kuma da baka. Gwanayen yaƙi ne, su dubu arba'in da huɗu, da ɗari bakwai da sittin ne (44,760).

19. Suka yi yaƙi da Hagarawa, da Yetur, da Nafish, da Nodab.

20. Aka taimake su yin yaƙi da abokan gābansu, sai aka ba da Hagarawa da duk waɗanda suke tare da su a hannunsu, saboda suka yi roƙo ga Allah a cikin yaƙin, Allah kuwa ya amsa musu roƙonsu saboda sun dogara gare shi.

21. Sai suka kwashe dabbobinsu, raƙuma dubu hamsin (50,000), da tumaki dubu ɗari biyu da dubu hamsin (250,000), da jakuna dubu biyu (2,000), da kuma mutane dubu ɗari (100,000).

22. Aka karkashe mutane da yawa, domin yaƙin na Allah ne. Sai suka gāje wurin zamansu, har lokacin da aka kai su bauta.

23. Mutanen rabin kabilar Manassa suna da yawa, sun zauna a ƙasar, daga Bashan har zuwa Ba'al-harmon, da Senir, da Dutsen Harmon.

24. Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu, Efer, da Ishi, da Eliyel, da Azriyel, da Irmiya, da Hodawiya, da Yadiyel. Su jarumawa ne na gaske, masu suna, su ne shugabannin gidajen kakanninsu.

Karanta cikakken babi 1 Tar 5