Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 29:4-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Na ba da zinariya tsantsa, talanti dubu uku (3,000), da azurfa tsantsa, talanti dubu bakwai (7,000), domin yin ado a bangon Haikalin,

5. da kuma dukan kayayyakin da masu sana'a za su yi. Yanzu fa ko akwai mai niyyar ba da sadaka ta yardar rai ga Ubangiji?”

6. Sa'an nan shugabannin gidajen kakanni, da shugabannin kabilai, da shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da aikin sarki, suka bayar da yardar rai.

7. Sun ba da zinariya talanti dubu biyar (5,000), da darik dubu goma (10,000), da azurfa talanti dubu goma (10,000), da tagulla talanti goma sha takwas (18,000), da ƙarfe talanti dubu ɗari (100,000).

8. Dukan waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka bayar da su cikin taskar Haikalin Ubangiji, ta hannun Yehiyel Bagershone.

9. Sai jama'a suka yi murna da ganin yadda suka bayar hannu sake, gama sun kawo sadakokinsu a gaban Ubangiji da zuciya ɗaya, shi sarki Dawuda kuma ya yi murna ƙwarai.

10. Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanmu Yakubu, yabo ya tabbata gare ka har abada abadin!

11. Girma, da iko, da daraja, da nasara, da ɗaukaka duk naka ne, ya Ubangiji, gama dukan abin da yake cikin sammai da duniya naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji. Kai ne Maɗaukaki duka.

12. Dukan wadata da girma daga gare ka suke, kai kake mulki da dukan iko da ƙarfi. Kai ne kake da iko ka ba mutum iko da ƙarfi.

13. Yanzu ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja.

14. “Amma wane ni ko kuma jama'ata, da za mu iya kawo sadaka mai yawa haka? Gama dukan kome daga gare ka yake. Daga cikin abin da muka karɓa daga wurinka muka ba ka.

15. Gama mu kamar baƙi ne, masu yawo a gabanka kamar kakanninmu. Kwanakinmu a duniya kamar inuwa ne, ba za mu tsere wa mutuwa ba.

16. Ya Ubangiji Allahnmu, duk wannan da muka kawo domin mu gina maka Haikali saboda sunanka mai tsarki, daga gare ka ne muka samu, duka naka ne.

Karanta cikakken babi 1 Tar 29