Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 29:22-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Sai suka ci, suka sha, suka yi murna a gaban Ubangiji a wannan rana.Sai suka sake shelar naɗin Sulemanu ɗan Dawuda sarki, a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa domin ya zama mai mulki na Ubangiji, Zadok kuwa shi ne firist.

23. Sai Sulemanu ya zauna a kan gādon sarauta na Ubangiji maimakon tsohonsa Dawuda. Ya yi nasara a cikin sarautar, Isra'ilawa dukansu suka yi masa biyayya.

24. Dukan ma'aikatan hukuma kuwa, da manyan mutane, da kuma dukan 'ya'yan sarki Dawuda, suka yi alkawari za su yi wa sarki Sulemanu biyayya.

25. Ubangiji kuwa ya ɗaukaka Sulemanu ƙwarai da gaske a gaban dukan Isra'ilawa, ya ɗaukaka sarautarsa fiye da ta waɗanda suka riga shi sarauta a Isra'ila.

26. Dawuda ɗan Yesse ya yi mulki bisa dukan Isra'ila,

27. har shekara arba'in. Ya yi mulki a Hebron shekara bakwai sa'an nan ya yi mulki shekara talatin da uku a Urushalima.

28. Sa'an nan ya rasu da kyakkyawan tsufa, cike da shekaru, da arziki, da daraja. Ɗansa Sulemanu kuma ya gāji sarautarsa.

29. An fa rubuta ayyukan sarki Dawuda daga farko har ƙarshe a tarihin Sama'ila, annabi, da na annabi Natan, da na annabi Gad.

30. An rubuta labarin mulkinsa, da ikonsa, da al'amuran da suka same shi, da Isra'ilawa, da dukan mulkokin ƙasashe na kewaye.

Karanta cikakken babi 1 Tar 29