Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 29:21-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Kashegari sai suka miƙa wa Ubangiji hadayu, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji, bijimai dubu ɗaya (1,000), da raguna dubu ɗaya (1,000), da 'yan raguna dubu ɗaya (1,000), da hadayunsu na sha, da hadayu masu yawa domin Isra'ila duka.

22. Sai suka ci, suka sha, suka yi murna a gaban Ubangiji a wannan rana.Sai suka sake shelar naɗin Sulemanu ɗan Dawuda sarki, a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa domin ya zama mai mulki na Ubangiji, Zadok kuwa shi ne firist.

23. Sai Sulemanu ya zauna a kan gādon sarauta na Ubangiji maimakon tsohonsa Dawuda. Ya yi nasara a cikin sarautar, Isra'ilawa dukansu suka yi masa biyayya.

24. Dukan ma'aikatan hukuma kuwa, da manyan mutane, da kuma dukan 'ya'yan sarki Dawuda, suka yi alkawari za su yi wa sarki Sulemanu biyayya.

25. Ubangiji kuwa ya ɗaukaka Sulemanu ƙwarai da gaske a gaban dukan Isra'ilawa, ya ɗaukaka sarautarsa fiye da ta waɗanda suka riga shi sarauta a Isra'ila.

26. Dawuda ɗan Yesse ya yi mulki bisa dukan Isra'ila,

27. har shekara arba'in. Ya yi mulki a Hebron shekara bakwai sa'an nan ya yi mulki shekara talatin da uku a Urushalima.

28. Sa'an nan ya rasu da kyakkyawan tsufa, cike da shekaru, da arziki, da daraja. Ɗansa Sulemanu kuma ya gāji sarautarsa.

Karanta cikakken babi 1 Tar 29