Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 29:16-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ya Ubangiji Allahnmu, duk wannan da muka kawo domin mu gina maka Haikali saboda sunanka mai tsarki, daga gare ka ne muka samu, duka naka ne.

17. Da yake na sani, ya Allahna, kakan gwada zuciya, kana ƙaunar gaskiya, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukan waɗannan abubuwa. Ina murna da ganin jama'arka waɗanda suke nan a tattare, sun kawo maka sadakokinsu da yardar rai.

18. Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kakanninmu, ka tabbatar da yardar rai ɗin nan a rayukan jama'arka, ka bi da zukatansu zuwa gare ka.

19. Ka kuma ba ɗana Sulemanu cikakkiyar zuciya, har da zai kiyaye umarnanka, da shaidunka, da dokokinka, domin ya aikata su duka, ya kuma gina Haikali wanda na riga na yi tanadi dominsa.”

20. Sa'an nan Dawuda ya ce wa taro duka, “Sai ku yabi Ubangiji Allahnku yanzu.” Taron jama'a kuwa suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu, suka rusuna har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada, suka kuma girmama sarki.

21. Kashegari sai suka miƙa wa Ubangiji hadayu, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji, bijimai dubu ɗaya (1,000), da raguna dubu ɗaya (1,000), da 'yan raguna dubu ɗaya (1,000), da hadayunsu na sha, da hadayu masu yawa domin Isra'ila duka.

22. Sai suka ci, suka sha, suka yi murna a gaban Ubangiji a wannan rana.Sai suka sake shelar naɗin Sulemanu ɗan Dawuda sarki, a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa domin ya zama mai mulki na Ubangiji, Zadok kuwa shi ne firist.

23. Sai Sulemanu ya zauna a kan gādon sarauta na Ubangiji maimakon tsohonsa Dawuda. Ya yi nasara a cikin sarautar, Isra'ilawa dukansu suka yi masa biyayya.

24. Dukan ma'aikatan hukuma kuwa, da manyan mutane, da kuma dukan 'ya'yan sarki Dawuda, suka yi alkawari za su yi wa sarki Sulemanu biyayya.

25. Ubangiji kuwa ya ɗaukaka Sulemanu ƙwarai da gaske a gaban dukan Isra'ilawa, ya ɗaukaka sarautarsa fiye da ta waɗanda suka riga shi sarauta a Isra'ila.

Karanta cikakken babi 1 Tar 29