Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 27:25-30-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25-30. Ga lissafin masu sarrafa dukiyar sarki.Ɗakin ajiya na sarki: Azmawet ɗan Adiyel,Ƙaramin ɗakin ajiya: Jonatan ɗan Uzziya,Aikin gona: Ezri ɗan Kabilu,Kurangar Inabi: Shimai daga Rama,Ɗakin ajiyar Inabi: Zabdi daga Shefam,Itatuwan zaitun da na ɓaure (a gindin tsaunukan yamma): Ba'al-hanan daga Geder,Ajiyar man zaitun: Yowash,Garken shanu na filin Sharon: Shirtai daga Sharon,Garken shanu na cikin kwari: Shafat ɗan Adlai,Raƙuma: Obil Ba'isma'ile,Jakuna: Yedaiya daga Meronot,Tumaki: Yaziz Bahagire.

31. Dukan waɗannan su ne masu lura da dukiyar sarki Dawuda.

32. Jonatan, kawun Dawuda, shi ne mai ba da shawara, yana da ganewa, shi kuma magatakarda ne. Shi da Yehiyel ɗan Hakmoni su ne masu koya wa 'ya'yan sarki, maza.

33. Ahitofel shi abokin shawarar sarki ne. Hushai Ba'arkite kuwa shi ne abokin sarki.

34. Sai Yehoyada ɗan Benaiya, da Abiyata suka gāji matsayin Ahitofel. Yowab shi ne babban shugaban sojojin sarki.

Karanta cikakken babi 1 Tar 27