Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 24:19-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Waɗannan suna da aikin da aka ba su na hidimar Haikalin Ubangiji bisa ga ka'idar da kakansu Haruna ya kafa musu, kamar yadda Ubangiji Allah na Isra'ila ya umarce shi.

20. Sauran 'ya'yan Lawi, maza, na wajen Amram, shi ne Shebuwel.Na wajen Shebuwel, shi ne Yedaiya.

21. Na wajen Rehabiya, shi ne Isshiya,

22. Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.

23. Na wajen Hebron, su ne Yeriya na fari, da Amariya, da Yahaziyel, da Yekameyam.

24. Na wajen Uzziyel, shi ne Mika, na wajen Mika, shi ne Shamir.

25. Ɗan'uwan Mika, shi ne Isshiya. Na wajen Isshiya, shi ne Zakariya.

26. Na wajen Merari, Mali da Mushi, da Yayaziya. Na wajen Yayaziya, shi ne Beno.

27. Na wajen Merari, wato na wajen Yayaziya, su ne Beno, da Shoham, da Zakkur, da Ibri.

28. Na wajen Mali, shi ne Ele'azara wanda ba shi da 'ya'ya maza.

29. Na wajen Kish, ɗan Kish, shi ne Yerameyel.

30. 'Ya'yan Mushi, maza, su ne Mali, da Eder, da Yerimot.Waɗannan su ne 'ya'yan Lawiyawa, maza, bisa ga gidajen kakanninsu.

31. Su ma suka jefa kuri'a kamar yadda 'yan'uwansu, 'ya'yan Haruna, maza, suka yi a gaban sarki Dawuda, da Zadok, da Ahimelek, da shugabannin gidajen kakanni na firistoci da na Lawiyawa. Shugaban gidan kakanni ya jefa kuri'a daidai da ƙanensa.

Karanta cikakken babi 1 Tar 24