Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 23:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. 'Ya'yan Libni, maza, su ne Yehiyel, shi ne babba, da Zetam, da Yowel, su uku.

9. 'Ya'yan Shimai, maza kuwa, su ne Shelomit, da Heziyel, da Haran, su uku. Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu, Libni.

10. 'Ya'yan Shimai, maza, su ne Yahat, da Zaina, da Yewush, da Beriya. 'Ya'yan Shimai, maza, ke nan, su huɗu.

11. Yahat shi ne babba, Zaina shi ne na biyu, amma Yewush, da Beriya ba su da 'ya'ya da yawa, saboda haka ana lasafta su a haɗe gida ɗaya.

12. 'Ya'yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel, su huɗu ke nan.

13. 'Ya'yan Amram, maza, su ne Haruna, da Musa. Aka keɓe Haruna domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, domin shi da 'ya'yansa za su ƙone turare a gaban Ubangiji, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.

14. Amma 'ya'yan Musa mutumin Allah, an lasafta su tare da kabilar Lawi.

15. 'Ya'yan Musa, maza, ke nan, Gershom da Eliyezer.

16. Ɗan Gershom babba shi ne Shebuwel.

Karanta cikakken babi 1 Tar 23