Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 21:4-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Duk da haka, sarki ya sa Yowab ya bi umarninsa. Sai Yowab ya tashi, ya bibiya ƙasar Isra'ila duka, sa'an nan ya komo Urushalima.

5. Yowab ya kawo wa Dawuda adadin yawan mutanen. Jimillar dukan Isra'ila zambar dubu ne da dubu ɗari (1,100,000) waɗanda za su iya yaƙi. Jimillar mutanen Yahuza kuwa dubu ɗari huɗu da dubu saba'in ne (470,000) waɗanda suka isa zuwa yaƙi.

6. Amma bai ƙidaya Lawiyawa da mutanen Biliyaminu ba, domin Yowab bai ji daɗin umarnin sarki ba.

7. Allah bai ji daɗin wannan al'amari ba, don haka sai ya bugi Isra'ila.

8. Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai saboda abin nan da na aikata. Amma ina roƙonka ka gafarta mini laifina, gama na yi aikin wauta ƙwarai da gaske.”

9. Sa'an nan Ubangiji ya yi magana da Gad, annabin Dawuda, ya ce,

10. “Je ka ka faɗa wa Dawuda, ka ce, ‘Ubangiji yana so ka zaɓi ɗaya daga cikin abu uku, wanda zai yi maka.’ ”

11. Gad kuwa ya tafi wurin Dawuda ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ka zaɓa,

12. ko shekara uku na yunwa, ko kuwa ka sha ɗibga a hannun maƙiyanka har wata uku, maƙiyanka su yi ta fafararka, ko kwana uku na takobin Ubangiji, wato annoba ke nan da zai aukar wa ƙasar, mala'ikan Ubangiji zai yi ta hallakarwa ko'ina a ƙasar Isra'ila. Yanzu fa, sai ka yi tunani, ka ba ni amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.”

13. Dawuda kuwa ya ce wa Gad, “Na shiga uku, gara in fāɗa a hannun Ubangiji, gama shi mai yawan jinƙai ne, kada ka bar ni in faɗa a hannun mutum.”

14. Saboda haka Ubangiji ya aiko da annoba a kan Isra'ila. Mutum dubu saba'in (70,000) na Isra'ila suka mutu.

15. Allah ya aiko mala'ikansa don ya hallaka Urushalima, amma sa'ad da yake gab da hallaka ta, sai Ubangiji ya gani, ya janye shirin annobar, ya ce wa mala'ikan hallakarwa, “Ya isa, janye hannunka.” Mala'ikan Ubangiji kuwa na tsaye kusa da masussukar Arauna Bayebuse.

16. Dawuda ya ɗaga idonsa, sai ya ga mala'ikan Ubangiji yana tsakanin sama da ƙasa, da takobinsa a zare a hannunsa a kan Urushalima. Sa'an nan Dawuda tare da dattawa suka fāɗi rubda ciki, suna saye da tufafin makoki.

17. Dawuda ya ce wa Allah, “Ai, ni ne na ba da umarni a ƙidaya jama'ar. Hakika, ni na yi zunubi, na kuwa aikata mummunan abu, amma waɗannan talakawa fa, me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, ka bar hannunka ya yi gāba da ni da gidan tsohona, amma kada ka yi gāba da jama'arka, har da za ka aukar musu da annoba.”

Karanta cikakken babi 1 Tar 21