Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 21:23-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Arauna ya ce wa Dawuda, “Ka karɓa, na ba ka, sai ka yi abin da kake so da ita, ranka ya daɗe. Zan kuma ba da bijimai domin hadayu na ƙonawa, in ba da keken sussuka domin itacen wuta, in kuma ba da alkama don hadaya ta gari. Zan ba ka waɗannan duka.”

24. Amma sarki Dawuda ya ce wa Arauna, “A'a, zan biya cikakken kuɗinta. Ba zan karɓi abinka kawai in ba Ubangiji ba, ba kuwa zan miƙa masa hadayu na ƙonawa da abin da ban biya ba.”

25. Sai Dawuda ya biya Arauna shekel ɗari shida na zinariya domin masussukar.

26. Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ya yi roƙo ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wutar da ta sauko daga sama a bisa bagaden hadayar ta ƙonawa.

27. Sa'an nan Ubangiji ya umarci mala'ikan, shi kuwa ya mai da takobinsa a kube.

28. Da Dawuda ya ga Ubangiji ya amsa masa a masussukar Arauna Bayebuse, sai ya miƙa hadaya a wurin.

29. Gama wurin zama na Ubangiji wanda Musa ya yi a jeji, da bagaden hadaya ta ƙonawa sun cikin masujada a Gibeyon.

30. Dawuda bai iya zuwa wurin don ya yi tambaya ga Allah ba, saboda yana jin tsoron takobin mala'ikan Ubangiji.

Karanta cikakken babi 1 Tar 21