Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 21:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Shaiɗan ya tashi gaba da Isra'ila, sai ya iza Dawuda ya ƙidaya Isra'ilawa.

2. Dawuda fa ya ce wa Yowab da sauran shugabannin jama'a, “Ku tafi, ku ƙidaya jama'ar Isra'ila tun daga Biyer-sheba har zuwa Dan, ku kawo mini labari don in san yawansu.”

3. Amma Yowab ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya yawan jama'arsa har sau ɗari bisa kan yadda suke a yanzu! Ranka ya daɗe, ya sarki, ashe, dukkansu ba naka ba ne? Me zai sa shugabana ya so a yi haka? Me zai sa ya zama sanadin tuntuɓe ga mutanen Isra'ila?”

4. Duk da haka, sarki ya sa Yowab ya bi umarninsa. Sai Yowab ya tashi, ya bibiya ƙasar Isra'ila duka, sa'an nan ya komo Urushalima.

5. Yowab ya kawo wa Dawuda adadin yawan mutanen. Jimillar dukan Isra'ila zambar dubu ne da dubu ɗari (1,100,000) waɗanda za su iya yaƙi. Jimillar mutanen Yahuza kuwa dubu ɗari huɗu da dubu saba'in ne (470,000) waɗanda suka isa zuwa yaƙi.

6. Amma bai ƙidaya Lawiyawa da mutanen Biliyaminu ba, domin Yowab bai ji daɗin umarnin sarki ba.

7. Allah bai ji daɗin wannan al'amari ba, don haka sai ya bugi Isra'ila.

8. Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai saboda abin nan da na aikata. Amma ina roƙonka ka gafarta mini laifina, gama na yi aikin wauta ƙwarai da gaske.”

Karanta cikakken babi 1 Tar 21