Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 2:17-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Abigail ta haifi Amasa. Mahaifin Amasa shi ne Yeter daga zuriyar Isma'ilu.

18. Azuba, matar Kalibu ɗan Hesruna ta haifa masa 'ya'ya maza. Matarsa Yeriyot kuma ta haifi 'ya'ya maza, su ne Yesher, da Shobab, da Ardon.

19. Sa'ad da Azuba ta rasu sai Kalibu ya auri Efrata wadda ta haifa masa Hur.

20. Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuwa shi ne mahaifin Bezalel.

21. Bayan haka sai Hesruna ya shiga wurin 'yar Makir mahaifin Gileyad, wadda ya aura sa'ad da yake da shekara sittin da haihuwa. Ta haifa masa Segub.

22. Segub shi ne mahaifin Yayir wanda yake da birane ashirin da uku a ƙasar Gileyad.

23. Amma sai Geshur da Aram suka ƙwace garuruwan Hawwotyayir ɗin daga gare su, har da Kenat da ƙauyukanta, garuruwa sittin. Duk waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.

24. Bayan rasuwar Hesruna, Abaija, matarsa, ta haifa masa Ashur, mahaifin Tekowa.

25. 'Ya'yan Yerameyel ɗan farin Hesruna, su ne Arama ɗan fari, sa'an nan Buna, da Oren, da Ozem, da Ahaija.

26. Sai Yerameyel ya auro wata mace, sunanta Atara. Ita ce mahaifiyar Onam.

27. 'Ya'yan Arama, ɗan farin Yerameyel, su ne Ma'az, da Yamin, da Eker.

28. 'Ya'yan Onam, maza, su ne Shammai da Yada. 'Ya'yan Shammai, maza, su ne Nadab da Abishur.

29. Sunan matar Abishur Abihail, ta haifa masa Aban da Molid.

30. 'Ya'yan Nadab, maza, su ne Seled da Affayim, amma Seled ya rasu bai bar 'ya'ya ba.

Karanta cikakken babi 1 Tar 2