Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 18:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sa'an nan Dawuda ya sa ƙungiyoyin sojoji a Suriya ta Dimashƙu, Suriyawa kuma suka zama bayin Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.

7. Dawuda kuma ya ƙwato garkuwoyi na zinariya waɗanda barorin Hadadezer suke ɗauke da su, ya kawo su Urushalima.

8. Dawuda kuma ya kwaso tagulla mai yawan gaske daga Beta da Berotayi, biranen Hadadezer. Da su ne Sulemanu ya yi kwatarniya, da ginshiƙai, da kayayyakin Haikali.

9. Sa'ad da Toyi, Sarkin Hamat, ya ji an ce Dawuda ya riga ya ci nasara a kan sojojin Hadadezer, Sarkin Zoba,

10. sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda, don ya gaishe shi, ya kuma yabe shi saboda ya yi yaƙi da Hadadezer, har ya ci shi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi. Adoniram kuwa ya kawo kayayyaki iri iri na zinariya, da na azurfa, da na tagulla.

Karanta cikakken babi 1 Tar 18