Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 18:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai Dawuda ya ƙwace karusai dubu (1,000), da mahayan dawakai dubu bakwai (7,000), da sojojin ƙasa dubu ashirin (20,000) daga gare shi. Dawuda kuma ya yanyanke agarar dawakan da suke jan karusai, amma ya bar waɗansu dawakai daga cikinsu waɗanda suka isa jan karusai ɗari.

5. Sa'ad da Suriyawa daga Dimashƙu suka zo don su taimaki Hadadezer Sarkin Zoba, sai Dawuda ya karkashe mutum dubu ashirin da dubu biyu (22,000) daga cikin Suriyawan.

6. Sa'an nan Dawuda ya sa ƙungiyoyin sojoji a Suriya ta Dimashƙu, Suriyawa kuma suka zama bayin Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.

7. Dawuda kuma ya ƙwato garkuwoyi na zinariya waɗanda barorin Hadadezer suke ɗauke da su, ya kawo su Urushalima.

8. Dawuda kuma ya kwaso tagulla mai yawan gaske daga Beta da Berotayi, biranen Hadadezer. Da su ne Sulemanu ya yi kwatarniya, da ginshiƙai, da kayayyakin Haikali.

Karanta cikakken babi 1 Tar 18