Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 16:24-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Ku yi shelar ɗaukakarsa ga al'ummai,Da ayyukansa masu girma ga dukan mutane,

25. Ubangiji da girma yake, wajibi ne mu yabe shi,Dole mu yi tsoronsa fiye da dukan alloli.

26. Gama allolin dukan sauran al'umma gumaka ne,Amma Ubangiji shi ne ya halitta sammai.

27. Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi,Iko da farin ciki sun cika haikalinsa.

28. Ku yi yabon Ubangiji, ku dukan mutanen duniya,Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!

29. Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja,Kuna kawo sadaka, kuna zuwa Haikalinsa.Ku rusuna a gaban Mai Tsarki da sahihiyar zuciya,

30. Ku yi rawar jiki a gabansa, ku dukan duniya!Hakika duniya ta kahu sosai, ba za ta jijjigu ba.

31. Duniya da sararin sama, ku yi farin ciki!Ku faɗa wa al'ummai, Ubangiji shi ne sarki.

32. Ki yi ruri, ke teku, da dukan abin da yake cikinki,Ka yi farin ciki, kai saura da dukan abin da yake cikinka.

33. Itatuwa a jeji za su yi sowa domin murnaSa'ad da Ubangiji zai zo ya yi mulki a duniya.

34. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne,Ƙaunarsa madawwamiya ce!

35. Ku ce masa, “Ka cece mu, ya Allah Mai Cetonmu,Ka tattara mu, ka kuɓutar da mu daga al'ummai,Domin mu gode maka,Mu kuma yabi sunanka mai tsarki.”

36. Ku yabi Ubangiji Allah na Isra'ila!Ku yi ta yabonsa har abada abadin!Sa'an nan dukan jama'a suka ce, “Amin, Amin,” suka yabi Ubangiji.

37. Dawuda ya sa Asaf tare da 'yan'uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji domin a yi hidima kullayaumin a gaban akwatin alkawarin kamar yadda aka bukaci a yi kowace rana.

38. Akwai kuma masu tsaron ƙofofi, wato Obed-edom ɗan Yedutun tare da 'yan'uwansa, su sittin da takwas, da Hosa.

Karanta cikakken babi 1 Tar 16