Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 15:23-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Berikiya da Elkana su ne masu tsaron ƙofa ta akwatin alkawari.

24. Sai Shebaniya, da Yehoshafat, da Netanel, da Amasai, da Zakariya, da Benaiya, da Eliyezer, firistoci, suka yi ta busa ƙaho a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-edom da Yehiya su ne kuma masu tsaron ƙofar akwatin alkawari.

25. Haka Dawuda, da dattawan Isra'ilawa, da shugabannin dubu dubu, suka tafi da murna domin su ɗauko akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-edom.

26. Saboda Allah ya taimaki Lawiyawa waɗanda suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi hadaya da bijimai bakwai da raguna bakwai.

27. Dawuda yana saye da kyakkyawar taguwa ta lilin tare da Lawiyawa duka waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, da mawaƙa, da Kenaniya shugaban mawaƙan. Dawuda kuma ya sa falmaran ta lilin.

28. Da haka fa Isra'ilawa duka suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suna ta sowa, suna ta busa ƙaho, suna kaɗa kuge da molaye, da garayu.

29. Sa'ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shigo birnin Dawuda, sai Mikal 'yar Saul ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana ta rawa, yana murna, sai ta ji ya saƙale mata a zuci.

Karanta cikakken babi 1 Tar 15