Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 15:2-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai Dawuda ya ce, “Kada wani ya ɗauki akwatin alkawari na Allah sai Lawiyawa kaɗai, gama su ne Ubangiji ya zaɓa domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su kuma yi masa hidima har abada.”

3. Saboda haka Dawuda ya tattara Isra'ilawa duka a Urushalima don a kawo akwatin alkawarin Ubangiji a wurinsa, inda aka riga aka shirya masa.

4. Dawuda kuma ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya, tare kuma da Lawiyawa.

5. Waɗanda aka tattaro ke nan, daga iyalin Kohat su ɗari da shirin ne. Uriyel shi ne shugabansu.

6. Daga iyalin Merari su ɗari biyu da ashirin, Asaya ne shugabansu.

7. Daga iyalin Gershon ɗari da talatin, Yowel ne shugabansu.

8. Daga iyalin Elizafan ɗari biyu, Shemaiya ne shugabansu.

9. Daga iyalin Hebron su tamanin, Eliyel ne shugabansu.

10. Daga iyalin Uzziyel ɗari da goma sha biyu, Amminadab ne shugabansu.

11. Sa'an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyata firistoci, da Lawiyawa, wato Uriyel, da Asaya, da Yowel, da Shemaiya, da Eliyel, da Amminadab,

12. ya ce musu, “Ku ne shugabanni na gidajen kakanninku, Lawiyawa. Sai ku tsarkake kanku da 'yan'uwanku domin ku iya kawo akwatin alkawarin Allah na Isra'ila a inda na shirya masa.

13. Gama Ubangiji Allahnmu ya fashe fushinsa a kanmu saboda ba ku ne kuka ɗauke shi a karo na farko ba, saboda kuma ba mu yi masa sujada kamar yadda aka umarta ba.”

14. Sa'an nan firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji Allah na Isra'ila.

15. Lawiyawa fa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah a bisa sandunansa a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.

16. Dawuda ya umarci shugabannin Lawiyawa su sa 'yan'uwansu mawaƙa su riƙa raira waƙa da murna, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, da molaye, da garayu, da kuge masu amon gaske.

Karanta cikakken babi 1 Tar 15