Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 13:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'an nan Dawuda ya yi shawara da shugabannin sojoji na dubu dubu da na ɗari ɗari, da kowane shugaba.

2. Ya kuma yi magana da dukan taron Isra'ilawa, ya ce, “Idan kun ga ya yi kyau, idan kuma nufin Ubangiji Allahnmu ne, to, bari mu aika a ko'ina wurin 'yan'uwanmu waɗanda aka rage a ƙasar Isra'ila, mu kuma aika wa firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a biranensu masu makiyaya domin su zo wurinmu.

3. Sa'an nan mu ɗauko akwatin alkawari na Allahnmu mu kawo shi wurinmu, gama mun ƙyale shi tun zamanin Saul.”

4. Jama'a kuwa suka amince da shawarar, suka yarda kuma a yi haka ɗin.

5. Haka fa, Dawuda ya tattara dukan Isra'ilawa wuri ɗaya, daga Shihor ta Masar, har zuwa mashigin Hamat domin a kawo akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim.

6. Sai Dawuda tare da dukan Isra'ilawa, suka haura zuwa Ba'al, wato Kiriyat-yeyarim ta Yahuza, domin su ɗauko akwatin alkawarin Allah daga can, inda ake kira bisa sunan Ubangiji, wanda kuma yake zaune a wurin kerubobi.

7. Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah a sabon keken shanu daga gidan Abinadab. Uzza da Ahiyo suka kora keken shanun.

Karanta cikakken babi 1 Tar 13