Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 12:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Waɗannan daga kabilar Gad shugabannin sojoji ne, waɗansu na mutum dubu, sauransu kuma ƙananan shugabanni ne waɗanda suke shugabancin sojoji ɗari.

15. Su ne waɗanda suka haye Urdun a watan fari na shekara, sa'ad da Kogin Urdun ɗin ya yi ambaliya. Suka kori waɗanda suke zaune a kwaruruka, na wajen gabas da yamma da kogin.

16. Sa'an nan waɗansu daga cikin mazajen Biliyaminu da na Yahuza, suka zo wurin Dawuda a kagararsa.

17. Sai Dawuda ya fito don ya tarye su, ya ce musu, “Idan da salama kuka zo wurina don ku taimake ni, to, zuciyata za ta zama ɗaya da taku, amma idan kun zo ne don ku bashe ni ga maƙiyana, to, Allah na kakanninmu ya duba ya shara'anta, da yake ba ni da laifi.”

18. Ruhun Allah kuwa ya sauko a kan Amasa wanda daga baya ya zama shugaban talatin ɗin, sai ya ce,“Muna tare da kai, ya Dawuda ɗan Yesse!Allah ya ba ka nasara tare da waɗanda suke tare da kai!Allah yana wajenka!”Sa'an nan Dawuda ya marabce su, ya maishe su shugabanni a sojojinsa.

19. Waɗansu sojoji daga Manassa, suka tafi wurin Dawuda sa'ad da yake fita tare da Filistiyawa don su yi yaƙi da Saul. Amma Dawuda bai tafi tare da su ba, domin sarakunan Filistiyawa sun yi shawara, suka sallame shi, don kada ya juya musu gindin baka, ya nemi sulhu a wurin shugabansu Saul, da kawunansu.

20. Sa'ad da yake komawa Ziklag sai sojojin Manassa suka zo wurinsa, wato su Adana, da Yozabad, da Yediyayel, da Maikel, da Yozabad, da Elihu, da Zilletai. A sojojin kabilar Manassa, waɗannan shugabannin sojoji ne na dubu dubu.

Karanta cikakken babi 1 Tar 12