Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 10:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ilawa, Isra'ilawa suka gudu a gaban Filistiyawa, aka karkashe su a Dutsen Gilbowa.

2. Filistiyawa suka kama Saul da 'ya'yansa maza, suka kashe Jonatan da Yishwi, da Malkishuwa.

3. Yaƙin ya tsananta wa Saul, maharba suka rutsa Saul, suka yi masa rauni.

4. Sai Saul ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Zare takobinka, ka kashe ni, don kada marasa kaciyan nan su zo su yi mini ba'a.” Amma mai ɗaukar makamai nasa bai yarda ba, gama yana jin tsoro ƙwarai. Saboda haka sai Saul ya zare takobinsa ya fāɗi a kansa.

5. Sa'ad da mai ɗaukar makamansa ya ga Saul ya mutu, sai shi ma ya faɗi a kan takobinsa ya mutu.

6. Ta haka Saul ya mutu, shi da 'ya'yansa maza guda uku tare da dukan gidansa.

7. Sa'ad da dukan Isra'ilawa waɗanda suke zaune a kwari suka ga sojojin sun gudu, Saul kuma da 'ya'yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa suka zo suka zauna a wurin.

8. Kashegari, sa'ad da Filistiyawa suka tafi su kwashe waɗanda aka kashe, sai suka tarar da Saul da 'ya'yansa maza matattu a Dutsen Gilbowa.

9. Suka kuwa tuɓe tufafinsa, suka datse kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka aiki manzanni ko'ina a ƙasar Filistiyawa don su ba gumakansu da jama'arsu wannan albishir.

Karanta cikakken babi 1 Tar 10