Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 7:31-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Bakinsa daga cikin dajiyar ya yi sama kamu guda. Bakin da'ira ne kamar fasalin gammo, kamu ɗaya da rabi. Akwai zāne-zāne a bakin. Sassan murabba'i ne, ba da'ira ba.

32. Ƙafafu huɗu ɗin, suna ƙarƙashin sassan. Sandunan ƙafafun a haɗe suke da dakalan. Tsayin kowace ƙafa kuwa kamu ɗaya da rabi ne.

33. Ƙafafun suna kama da ƙafafun karusa. Sandunan ƙafafun, da gyaffansu, da kome na ƙafafun duka na zubi ne.

34. Akwai ginshiƙi huɗu daga ƙarƙashin kowane dakali. Ginshiƙan suna haɗe da dakalan.

35. Akwai wani abu kamar gammo mai tsayi rabin kamu a kan dakalin. Ginshiƙan kuma da sassan a haɗe suke da dakalin.

36. Ya zana siffofin kerubobi, da na zakoki, da na itatuwan dabino a jikin ginshiƙan da sassan a duk inda ya ga akwai fili. Ya kuma zana furanni kewaye da su.

37. Haka aka yi dakalai, dukansu iri ɗaya ne, girmansu da fasalinsu kuma iri ɗaya ne.

38. Ya kuma yi daruna na tagulla guda goma. Kowane daro yana cin misalin garwa tamanin. Kowane daro kamu huɗu ne. Kowane dakali yana da daro ɗaya.

39. Ya kafa dakali biyar a gefen dama na Haikalin, ya kuma kafa biyar a gefen hagu na Haikalin. Ya kuma sa kwatarniya na zubi a gefen dama na Haikalin, wajen kusurwar gabas maso kudu.

40-45. Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe da manyan cokula, da daruna. Haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sulemanu a cikin Haikalin Ubangiji. Ga abin da ya yi.ginshiƙai biyudajiya da take a kawunan ginshiƙanraga biyu don rufe dajiyar da take akawunan ginshiƙaisiffofin rumman ɗari huɗu dominraga biyu ɗin, da jeri biyu nasiffofin rumman domin kowaceraga don a rufe dajiyar da take akawunan ginshiƙandakalai gomadaruna goma a kan dakalankwatarniya ɗayasiffofin bijimai guda goma sha biyuda kwatarniya take zaune a kai,tukwanen ƙarfe, da manyan cokula,da kwanoniDukan kayayyakin aiki a cikin Haikalin Ubangiji waɗanda Huram ya yi wa sarki Sulemanu, an yi su ne da gogaggiyar tagulla.

46. Sarki ya sa a yi zubinsu a filin Urdun a ƙasar yumɓun da yake tsakanin Sukkot da Zaretan.

47. Sulemanu bai auna nauyin kayayyakin aikin ba domin sun cika yawa. Ba a kuma san nauyin tagullar ba.

48-50. Sulemanu ya yi dukan kayayyakin aikin da suke na Haikalin Ubangiji.bagaden zinariyateburin zinariya inda ake ajiyegurasar ajiyewaalkuki na zinariya guda biyar a gefendama, biyar kuma a gefen hagu agaban Wuri Mafi Tsarki na cancikifurannifitiluarautakifinjalai na zinariyahantsukadarunacokulafarantan wuta na zinariya tsantsaalmanani na zinariya domin ƙofofinɗaki na can cikin Haikali, watoWuri Mafi Tsarki, da ƙofofinHaikalin

51. Haka sarki Sulemanu ya gama dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sai ya kawo abubuwan da tsohonsa Dawuda ya keɓe, wato azurfa, da zinariya, da kayayyakin aiki, ya ajiye su cikin taskokin Haikalin Ubangiji.

Karanta cikakken babi 1 Sar 7