Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 4:25-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka zauna lafiya tun daga Dan har Biyersheba. Kowa ya yi zamansa a gida dukan kwanakin Sulemanu.

26. Sulemanu kuma yana da rumfuna dubu arba'in (40,000) domin dawakan karusansa, da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000).

27. Hakiman nan nasa sha biyu, kowa ya kawo wa Sulemanu abinci, duk da waÉ—anda suke zuwa teburin cin abincin Sulemanu. Kowane hakimi yakan kawo abincin da za a ci na wata guda. Ba su fasa kawowa ba.

28. Suka kuma kawo sha'ir da ingirci domin dawakan da suke jan karusai, da sauran dabbobin da suke aiki. Kowanne bisa ga abin da aka sa masa.

29. Allah ya ba Sulemanu hikima, da fahimi, da sani, har ba su misaltuwa.

Karanta cikakken babi 1 Sar 4