Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Fādawan Sulemanu

1. Sarki Sulemanu shi ne sarkin dukan Isra'ila,

2-6. waɗannan kuma su ne manyan fādawansa,Azariya ɗan Zadok shi ne firist.Elihoref da Ahija 'ya'yan Seraiya,maza, su ne magatakarda.Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne mailura da takardu.Benaiya ɗan Yehoyada shi neshugaban sojoji.Zadok da Abiyata su ne firistoci.Azariya ɗan Natan shi ne shugabanhakimai.Zabud ɗan Natan shi ne mashawarcinsarki da abokinsa.Ahishar shi ne mai lura da bayin fāda.Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lurada aikin gandu.

7. Sulemanu kuma ya naɗa mutum goma sha biyu a lardunan Isra'ila. Su ne za su tanaji abinci daga lardunansu domin sarki da iyalinsa. Kowane hakimi yakan kawo abinci wata guda a shekara.

8-19. Waɗannan su ne hakimai, da kuma lardunan da suke aiki.Ben-hur yana a ƙasar tudu ta Ifraimu.Ben-deker shi ne mai lura da biranenMakaz, da Shalim, da Bet-shemesh,da Elon-bet-hanan.Ben-hesed shi ne mai lura da Arubot,da Soko, da dukan ƙasar Hefer.Ben-abinadab shi ne mai lura dadukan jihar Dor, ya auri Tafat'yar Sulemanu.Ba'ana ɗan Ahilud shi ne mai lura dabiranen Ta'anak da Magiddo, dadukan jihar Bet-sheyan, kusa dagarin Zaretan, kudu da garinYezreyel, har zuwa birnin Abelmehola da birnin Yokmeyam.Ben-geber shi ne mai fura da birninRamot-gileyad, da ƙauyukanYayir da Manassa, waɗanda suke aGileyad, da kuma yankin Argob,wanda yake a Bashan, duka daiakwai manyan garuruwa sittinmasu garu da ƙyamare na tagulla.Abinadab ɗan Iddo shi ne mai lurada birnin Mahanayim.Ahimawaz shi ne mai lura da Naftali,ya auri Basemat 'yar Sulemanu.Ba'ana ɗan Hushai shi ne mai lurada Ashiru da garin Beyalot.Jehoshafat ɗan Faruwa shi ne mailura da Issaka.Shimai ɗan Ila shi ne mai lura daƙasar Biliyaminu.Geber ɗan Uri shi ne mai lura dajihar Gileyad wadda Sihon SarkinAmoriyawa, da Og Sarkin Bashan,suka mallaka.Bayan waɗannan sha biyu akwai hakimi ɗaya da yake kan ƙasar Yahuza.

Hikimar Sulemanu da Wadatarsa

20. Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka yi yawa kamar yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka yi murna.

21. Sulemanu ya sarauci dukan mulkoki tun daga Kogin Yufiretis a gabas, har zuwa ƙasar Filistiyawa a yamma, daga kudu kuma har zuwa iyakar Masar. Su kuwa suka yi ta kawo wa Sulemanu harajinsu, ya kuwa mallake su dukan kwanakin ransa.

22. Abincin gidan Sulemanu na rana ɗaya garwa talatin na lallausan gari ne, da garwa sittin na gari,

23. da turkakkun bijimai goma, da shanu ashirin daga makiyaya, da tumaki ɗari banda kishimai, da bareyi, da batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.

24. Sulemanu ya mallaki dukan ƙasar da yake yamma da Kogin Yufiretis, daga Tifsa har zuwa birnin Gaza. Ya mallaki dukan sarakuna yammacin Yufiretis. Akwai zaman lafiya ko'ina a mulkinsa da ƙasashen maƙwabta.

25. Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka zauna lafiya tun daga Dan har Biyersheba. Kowa ya yi zamansa a gida dukan kwanakin Sulemanu.

26. Sulemanu kuma yana da rumfuna dubu arba'in (40,000) domin dawakan karusansa, da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000).

27. Hakiman nan nasa sha biyu, kowa ya kawo wa Sulemanu abinci, duk da waɗanda suke zuwa teburin cin abincin Sulemanu. Kowane hakimi yakan kawo abincin da za a ci na wata guda. Ba su fasa kawowa ba.

28. Suka kuma kawo sha'ir da ingirci domin dawakan da suke jan karusai, da sauran dabbobin da suke aiki. Kowanne bisa ga abin da aka sa masa.

29. Allah ya ba Sulemanu hikima, da fahimi, da sani, har ba su misaltuwa.

30. Hikimar Sulemanu ta fi ta dukan mutanen gabas, ko masu hikima na Masar.

31. Gama ya fi dukan mutane hikima, ya fi Etan Ba'ezrahe, da Heman, da Kalkol, da Darda, 'ya'yan Mahol. Ya shahara a ƙasashen da suke kewaye da shi.

32. Ya yi karin magana dubu uku, ya kuma yi waƙoƙi fiye da dubu.

33. Ya yi magana a kan itatuwa da tsire-tsire tun daga itacen al'ul da yake a Lebanon har zuwa ɗaɗɗoya da take tsirowa a jikin bango. Ya kuma yi magana a kan dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kifaye.

34. Sarakuna daga ko'ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.