Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 4:21-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sulemanu ya sarauci dukan mulkoki tun daga Kogin Yufiretis a gabas, har zuwa ƙasar Filistiyawa a yamma, daga kudu kuma har zuwa iyakar Masar. Su kuwa suka yi ta kawo wa Sulemanu harajinsu, ya kuwa mallake su dukan kwanakin ransa.

22. Abincin gidan Sulemanu na rana ɗaya garwa talatin na lallausan gari ne, da garwa sittin na gari,

23. da turkakkun bijimai goma, da shanu ashirin daga makiyaya, da tumaki ɗari banda kishimai, da bareyi, da batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.

24. Sulemanu ya mallaki dukan ƙasar da yake yamma da Kogin Yufiretis, daga Tifsa har zuwa birnin Gaza. Ya mallaki dukan sarakuna yammacin Yufiretis. Akwai zaman lafiya ko'ina a mulkinsa da ƙasashen maƙwabta.

25. Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka zauna lafiya tun daga Dan har Biyersheba. Kowa ya yi zamansa a gida dukan kwanakin Sulemanu.

26. Sulemanu kuma yana da rumfuna dubu arba'in (40,000) domin dawakan karusansa, da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000).

27. Hakiman nan nasa sha biyu, kowa ya kawo wa Sulemanu abinci, duk da waɗanda suke zuwa teburin cin abincin Sulemanu. Kowane hakimi yakan kawo abincin da za a ci na wata guda. Ba su fasa kawowa ba.

28. Suka kuma kawo sha'ir da ingirci domin dawakan da suke jan karusai, da sauran dabbobin da suke aiki. Kowanne bisa ga abin da aka sa masa.

29. Allah ya ba Sulemanu hikima, da fahimi, da sani, har ba su misaltuwa.

30. Hikimar Sulemanu ta fi ta dukan mutanen gabas, ko masu hikima na Masar.

31. Gama ya fi dukan mutane hikima, ya fi Etan Ba'ezrahe, da Heman, da Kalkol, da Darda, 'ya'yan Mahol. Ya shahara a ƙasashen da suke kewaye da shi.

32. Ya yi karin magana dubu uku, ya kuma yi waƙoƙi fiye da dubu.

33. Ya yi magana a kan itatuwa da tsire-tsire tun daga itacen al'ul da yake a Lebanon har zuwa ɗaɗɗoya da take tsirowa a jikin bango. Ya kuma yi magana a kan dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kifaye.

34. Sarakuna daga ko'ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.

Karanta cikakken babi 1 Sar 4