Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 3:20-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Da tsakar daren sai ta tashi, ta ɗauke ɗana daga wurina, sa'ad da nake barci, ta kai shi gadonta, sa'an nan ta kwantar da mataccen ɗanta a wurina.

21. Sa'ad da na tashi da safe don in ba ɗana mama, sai ga shi, matacce. Da na duba sosai, sai na ga ba nawa ba ne, wanda na haifa.”

22. Amma ɗaya matar ta ce, “A'a, mai ran shi ne nawa, mataccen kuwa shi ne naki!”Sai ta fari ta ce, “A'a, mataccen shi ne naki, mai rai ne nawa!”Haka suka yi ta gardama a gaban sarki.

23. Sa'an nan sarki ya ce, “To, kowaccenku ta ce mai ran shi ne nata, mataccen kuwa shi ne na waccan.”

24. Sai ya umarta a kawo takobi. Da aka kawo takobin,

25. sai ya ce, “A raba ɗan nan mai rai kashi biyu, kowacce ta ɗauki rabi.”

26. Saboda zuciyar mahaifiyar ta ainihi ta cika da juyayin ɗanta, ta ce wa sarki, “Ranka ya daɗe kada a kashe yaron! A ba ta!”Amma ɗayar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu, a ci gaba a raba shi.”

27. Sa'an nan Sulemanu ya ce, “Kada ku kashe yaron! Ku miƙa wa ta farin, ita ce mahaifiyarsa ta ainihi.”

28. Sa'ad da dukan mutanen Isra'ila suka ji shari'ar da sarki ya yanke, sai suka girmama shi ƙwarai, gama sun gane Allah ya ba shi hikimar daidaita husuma sosai.

Karanta cikakken babi 1 Sar 3