Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 22:35-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. A ran nan yaƙi ya yi tsanani. Aka tallafi Ahab a cikin karusarsa a gaban Suriyawa. Da maraice ya mutu. Jinin raunin da aka yi masa ya zuba a cikin karusar.

36. A wajen faɗuwar rana aka yi wa sojoji shela aka ce, “Kowa ya koma garinsu da ƙasarsu.”

37. Sarki Ahab ya mutu, aka kawo shi Samariya, aka binne shi.

38. Suka wanke karusarsa a tafkin Samariya. Karnuka suka lashe jininsa, karuwai kuma suka yi wanka a tafkin kamar yadda Ubangiji ya faɗa.

39. Sauran ayyukan Ahab da dukan abin da ya yi, da gidan da ya gina na hauren giwa da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

40. Ahab ya rasu kamar kakanninsa. Ɗansa Ahaziya ya gāji sarautarsa.

41. Yehoshafat ɗan Asa ya ci sarautar Yahuza a shekara ta huɗu ta sarautar Ahab, Sarkin Isra'ila.

42. Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara ashirin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Azuba 'yar Shilhi.

43. Ya bi halin tsohonsa, Asa, bai karkace ba. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Duk da haka ba a rushe wuraren tsafin na tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu, suka ƙona turare a tuddan.

44. Yehoshafat kuma ya ba Sarkin Isra'ila amana.

45. Sauran ayyukan Yehoshafat, da ƙarfin da ya nuna, da yadda ya yi yaƙi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

46. Ya kori dukan karuwai mata da maza da suka ragu a ƙasar a zamanin tsohonsa Asa.

47. A lokacin babu sarki a Edom sai wakili.

Karanta cikakken babi 1 Sar 22