Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 2:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Don haka dole ka hukunta shim, ka dai san abin da za ka yi da shi, lalle ne kuma za ka ga an kashe shi.”

10. Sa'an nan Dawuda ya rasu, aka binne shi a birnin Urushalima.

11. Ya yi shekara arba'in yana sarautar Isra'ila. Ya yi mulki shekara bakwai a Hebron, sa'an nan ya yi shekara talatin da uku yana mulki a Urushalima.

12. Sulemanu kuwa ya hau gadon sarautar ubansa, Dawuda. Mulkinsa kuma ya kahu sosai.

13. Sa'an nan Adonija ɗan Haggit ya tafi wurin Bat-sheba, tsohuwar Sulemanu. Ta ce masa, “Ka zo lafiya?”Ya ce, “Lafiya lau.”

14. Sa'an nan ya ce, “Ina da wani abin da zan faɗa miki.”Ta ce, “To, sai ka faɗa.”

15. Ya amsa ya ce, “Kin sani dai sarauta tawa ce. Ni ne kuwa mutanen Isra'ila duka suka sa zuciya zan ci sarautar, amma al'amarin ya sāke, sai sarautar ta zama ta ƙanena , gama tasa ce bisa ga nufin Allah.

16. Yanzu dai ina da roƙo guda zuwa gare ki, kada ki hana mini.”

Karanta cikakken babi 1 Sar 2