Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 18:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Obadiya ya ce, “Wane laifi na yi, har da za ka ba da ni a hannun Ahab ya kashe ni?

10. Na rantse da Ubangiji Allahnka mai rai, ba al'umma ko mulki da shugabana sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka nan, sai ya sa mulkin ko al'ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba.

11. Yanzu kuwa ka ce, in tafi in faɗa masa, cewa ga ka a nan?

12. Rabuwata da kai ke da wuya, sai Ruhun Ubangiji ya kai ka wurin da ban sani ba, don haka, in na tafi na faɗa wa Ahab, in bai same ka ba, to, ni zai kashe, ko da yake ni baranka, tun ina saurayi nake tsoron Ubangiji.

13. Ashe, ba ka ji ba? Na kasa annabawan Ubangiji biyu, na ɓoye su a kogo hamsin hamsin, sa'ad da Yezebel ta kashe annabawan Ubangiji, na ciyar da su, na kuma shayar da su.

14. Yanzu kuwa ka ce, in tafi in faɗa wa sarki Ahab, cewa ga ka nan, ai, zai kashe ni.”

15. Iliya kuwa ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji Mai Runduna, wanda nake tsaye a gabansa, hakika zan nuna kaina gare shi yau.”

16. Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya.

17. Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne, wanda kake wahalar da Isra'ila?”

Karanta cikakken babi 1 Sar 18