Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 18:36-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. A lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai annabi Iliya ya matso kuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila, bari ya zama sananne a wannan rana, cewa kai ne Allah a Isra'ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa duka bisa ga maganarka.

37. Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, domin waɗannan mutane su sani, kai Ubangiji, kai ne Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu.”

38. Ubangiji kuwa ya sa wuta ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsun, da ƙurar, ta kuma lashe ruwan da yake cikin wuriyar.

39. Sa'ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka rusuna suka sunkuyar da kai suka ce, “Ubangiji shi ne Allah, Ubangiji shi ne Allah.”

40. Iliya kuma ya ce musu, “Ku kama annabawan Ba'al, kada ku bar ko ɗaya ya tsere.” Iliya kuwa ya kai su rafin Kishon, ya karkashe su a can.

41. Iliya kuwa ya ce wa Ahab, “Sai ka haura ka ci ka sha, gama akwai motsin sakowar ruwan sama.”

42. Sai Ahab ya haura don ya ci ya sha, Iliya kuwa ya hau can ƙwanƙolin Karmel, ya zauna ƙasa, ya haɗa kai da gwiwa.

Karanta cikakken babi 1 Sar 18