Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 16:20-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sauran ayyukan Zimri da makircin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

21. Jama'ar Isra'ila suka rabu biyu. Rabi suka bi Tibni ɗan Ginat don su naɗa shi sarki. Rabin kuwa suka bi Omri.

22. Amma jama'ar da suka bi Omri suka rinjayi waɗanda suka bi Tibni ɗan Ginat. Sai Tibni ya mutu, Omri kuwa ya zama sarki.

23. A shekara ta talatin da ɗaya ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Omri ya ci sarautar Isra'ila. Ya yi shekara goma sha biyu yana sarauta. Ya yi shekara shida yana mulki a Tirza.

24. Sa'an nan ya sayi tudun Samariya daga Shemer a bakin azurfa dubu shida (6,000), a wurin Shemer, ya kuwa yi gini a kan tudun, ya sa masa suna Samariya saboda sunan Shemer mai tudun.

25. Omri kuwa ya aikata mugunta a gaban Ubangiji fiye da dukan waɗanda suka riga shi.

26. Ya bi duk irin hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat, da irin zunuban da ya sa jama'ar Isra'ila su yi. Suka sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi saboda gumakansu.

27. Sauran ayyukan da Omri ya yi, da kama-karyar da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

28. Omri kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Ɗansa Ahab ya gāji sarautarsa.

29. A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ahab ɗan Omri ya yi sarautar Isra'ila. Ahab ɗan Omri kuwa ya yi sarautar Isra'ila a Samariya shekara ashirin da biyu.

30. Shi kuma ya aikata mugunta a gaban Ubangiji fiye da dukan waɗanda suka riga shi.

31. Da yake abu ne mai sauƙi a gare shi ya bi hanyar zunuban Yerobowam ɗan Nebat, sai ya auro Yezebel 'yar Etba'al, Sarkin Sidon, ya kuma bauta wa gunkin nan Ba'al, ya yi masa sujada.

32. Ya gina wa Ba'al bagade a matsafar Ba'al ɗin, da ya gina a Samariya.

33. Ahab kuma ya yi gunkiyan nan Ashtoret. Ahab dai ya yi abin da ya sa Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra'ila waɗanda suka riga shi.

34. A cikin kwanakinsa, Hiyel mutumin Betel ya gina Yariko. Ya yi hasarar ɗan farinsa, Abiram, sa'ad da ya kafa harsashin ginin, ya kuma yi hasarar autansa, Segub, sa'ad da ya sa ƙofofin, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Joshuwa ɗan Nun.

Karanta cikakken babi 1 Sar 16