Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 14:4-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Matar kuwa ta yi haka. Ta tashi ta tafi Shilo a gidan Ahija. Ahija ba ya gani, saboda tsufa.

5. Ubangiji ya ce wa Ahija, “Ga matar Yerobowam tana zuwa don ta tambaye ka abin da zai faru da ɗanta, gama ɗan yana ciwo. To, da haka za ka amsa mata, gama sa'ad da ta zo, za ta nuna kamar ita wata mace ce dabam.”

6. Da Ahija ya ji motsin takawarta a bakin ƙofa, sai ya ce mata, “Ki shigo, matar Yerobowam, me ya sa kike yi kamar ke wata ce dabam? Gama an umarce ni in faɗa miki labari marar daɗi.

7. Ki koma, ki faɗa wa Yerobowam, Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Na ɗaukaka ka daga cikin mutane, na sa ka zama shugaban mutanena, Isra'ilawa.

8. Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba ka, duk da haka ba ka zama kamar bawana Dawuda ba, wanda ya kiyaye umarnaina, ya bi ni da zuciya ɗaya, yana yin abin da yake daidai a gare ni.

9. Amma ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka riga ka, ka yi wa kanka gumaka, da siffofi na zubi, ka tsokane ni in yi fushi, ka yi watsi da ni.

10. Saboda haka zan kawo masifa a gidanka. Zan datse maka kowane ɗa namiji, ko bawa, ko 'yantacce, daga cikin Isra'ila. Zan ƙone gidanka kamar yadda akan ƙone juji ƙurmus.

11. Duk wanda yake naka wanda zai mutu a birni, karnuka za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura tsuntsaye za su cinye shi, ni Ubangiji, ni ne na faɗa.’

12. “Ki tashi, ki koma gida. Da shigarki birni, yaron zai mutu.

13. Dukan jama'ar Isra'ila za su yi makoki dominsa, su binne shi, gama shi kaɗai zai sami binnewa daga cikin gidan Yerobowam, domin a gare shi kaɗai aka iske abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, yake murna da shi.

14. Ubangiji kuma zai ta da wani wanda zai sarauci Isra'ila, wanda kuma zai rushe gidan Yerobowam daga yanzu har zuwa nan gaba.

15. Ubangiji zai hukunta Isra'ila kamar yadda akan girgiza iwa a baƙin rafi, zai tumɓuke Isra'ila daga wannan ƙasa mai albarka wadda ya ba kakanninsu, ya kuma watsar da su a hayin Kogin Yufiretis, domin sun yi wa kansu gumaka don sun tsokani Ubangiji ya yi fushi.

16. Ubangiji zai rabu da Isra'ila saboda zunuban Yerobowam waɗanda ya yi, da kuma waɗanda ya sa mutanen Isra'ila su yi.”

17. Sa'an nan matar Yerobowam ta tashi, ta tafi Tirza. Amma tana shiga gidan ke nan, sai yaron ya mutu.

18. Jama'ar Isra'ila duka suka binne shi, suka yi makoki dominsa, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa, annabi Ahija.

19. Sauran ayyukan Yerobowam, da yaƙe-yaƙensa, da yadda ya yi mulki, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

Karanta cikakken babi 1 Sar 14