Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 11:22-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Amma Fir'auna ya ce masa, “Me ka rasa a nan har da kake so ka koma ƙasarka?”Hadad ya ce masa, “Ka dai yardar mini kawai in tafi.” Ya kuwa koma ƙasarsa.

23. Allah kuma ya sa Rezon ɗan Eliyada, ya tayar wa Sulemanu, shi Rezon ya gudu daga wurin maigidansa, Hadadezer Sarkin Zoba.

24. Ya tattara wa kansa mutane ya zama shugaban 'yan hari bayan kashe-kashen da Dawuda ya yi. Sai suka tafi Dimashƙu, suka zauna a can, suka naɗa shi Sarkin Dimashƙu.

25. Ya zama abokin gāban Isra'ila a dukan zamanin Sulemanu. Ya yi ta ɓarna kamar yadda Hadad ya yi. Ya ƙi jinin mutane Isra'ila. Ya yi mulkin suriya.

26. Sai Yerobowam ɗan Nebat, Ba'ifraime na Zaretan, baran Sulemanu, wanda sunan mahaifiyarsa Zeruya, wadda mijinta ya rasu, shi ma ya tayar wa sarki.

27. Ga dalilin da ya sa ya tayar wa sarki.Sulemanu ya gina Millo ya kuma faɗaɗa garun birnin Dawuda tsohonsa.

28. Yerobowam mutum ne mai fasaha. Da Sulemanu ya ga shi saurayi ne mai himma, sai ya shugabantar da shi kan aikin tilas na gidan Yusufu.

29. A sa'ad da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahija mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahija yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai,

30. sai Ahija ya kama sabuwar rigar da ya sa, ya kyakketa ta ƙyalle goma sha biyu,

31. ya ce wa Yerobowam, “Kwashi ƙyalle goma, gama haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, ina gab da in kece sarauta daga hannun Sulemanu, zan ba ka kabila goma.

32. Amma Sulemanu, zai sami kabila ɗaya saboda bawana Dawuda, da kuma ɗaya saboda Urushalima, wato birnin da na zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka.

33. Domin Sulemanu ya rabu da ni, ya bauta wa Ashtoret, gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh, gunkin Mowab, da Milkom, gunkin Ammonawa. Bai yi tafiya a cikin tafarkuna ba, bai yi abin da yake daidai a gare ni ba, bai kiyaye dokokina, da ka'idodina kamar yadda Dawuda, tsohonsa, ya yi ba.

34. Duk da haka ba zan karɓe sarauta duka daga hannunsa ba, amma zan bar shi ya yi mulki muddin ransa saboda bawana Dawuda, wanda na zaɓa, wanda ya kiyaye umarnaina da dokokina.

35. Amma zan karɓe mulki daga hannun ɗansa in ba ka, zan ba ka kabila goma.

Karanta cikakken babi 1 Sar 11