Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 1:15-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Bat-sheba kuwa ta tafi wurin sarki a ɗakinsa. Sarki dai ya tsufa ƙwarai, Abishag, yarinyar nan daga Shunem, tana yi masa hidima.

16. Bat-sheba ta rusuna, ta gai da sarki. Sai sarki ya ce mata, “Me kike so?”

17. Ta ce masa, “Ranka ya daɗe, ka riga ka rantse mini da sunan Ubangiji Allahnka, ka ce, ‘Sulemanu ɗanki zai yi mulki bayana, shi ne zai hau gadon sarautata.’

18. To, ga shi Adonija ya zama sarki, ko da yake kai ba ka sani ba.

19. Ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Abiyata firist, da Yowab shugaban sojoji, amma bai gayyaci Sulemanu ɗanka ba.

20. Ranka ya daɗe, yanzu idanun dukan jama'ar Isra'ila suna kallonka don su ga wanda za ka nuna musu ya gāji gadon sarauta a bayanka.

21. In ba haka ba, zai zama sa'ad da ka rasu za a ɗauka ni da ɗana, sulemanu, masu laifi ne.”

22. Tana cikin magana da sarki, sai annabi Natan ya zo.

23. Aka faɗa wa sarki cewa, ga annabi Natan. Da ya zo gaban sarki, sai ya rusuna ya gaishe shi.

24. Sa'an nan ya ce, “Ranka ya daɗe, ashe, ko ka sanar, cewa Adonija ne zai gaje ka?

25. Gama yau ɗin nan ya tafi ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Yowab shugaban sojoji, da Abiyata firist. Ga shi, suna ci suna sha tare da shi, suna cewa, ‘Ran sarki Adonija ya daɗe.’

26. Amma ni da Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da ɗanka Sulemanu, bai gayyace mu ba.

27. Ranka ya daɗe ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fādawanka, cewa ga wanda zai gāje ka ba?”

Karanta cikakken babi 1 Sar 1